Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, (mai ritaya), ya bayyana dalilin da ya sa ta’addanci, ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Najeriya ke da wuya a magance su.

Da yake jawabi a wani taro da aka shirya a Jihar Legas, kan bikin ranar Demokradiya ta 12 ga Yuni, Janar Musa ya ce matsalar na ci gaba da wanzuwa a wani bangare na kasar saboda kungiyoyin ’yan ta’adda na samun goyon baya daga wasu mutane a cikin al’ummomin yankunan.

“’Yan bindiga, ’yan tawaye, ta’addanci. Me yasa yake da wuya a magance shi? Watakila, muna da mutanen da su ma suke karfafa gwiwa da kuma ba da goyon baya ga wadannan abubuwa su faru saboda ’yan ta’adda, ’yan bindiga, suna rayuwa ne a tsakanin mutanen.

“Akwai labarai da dama na yadda mutane suka taimaka musu wajen ba su abinci, ba su ruwa, da kuma ba su bayani, kuma waɗannan su ne abubuwan da ke ci gaba da ba su karfi.”

Tsohon Hafsan Tsaron ya nuna cewa sojoji da sauran hukumomin tsaro ba za su iya cin galaba kan rashin tsaro ba tare da hadin kan ’yan kasa ba, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su rika bayar da rahoton ayyukan da ake zargi da kuma ba da goyon baya ga kokarin tsaro da ake yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *