Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya bayyana cewa za a binne Marigayi jagoran gwamnatin juyin juya halin Iran, Ali Khamenei, a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli.
Hukumomi a Tehran sun ce za’a fara ne hidimar jana’izar marigayin ne tun daga ranar 4 ga watan na Yuli, har zuwa ranar 9 ga wata, da za’ayi dafifin raka Jagoran zuwa masaukin sa na din-din-din dake Makwancin Imam Reza (Mashhad).
- DRC: Zanga-zangar adawa da shirin canza kundin tsarin mulki ta rikide zuwa tashin hankali
- Dalilan da ya sa aka kasa magance matsalar tsaro — Janar Musa
An kashe Khamenei ne a ranar 28 ga Fabarairun shekarar 2026, yayin wani hari da Amurka da Israila suka kai kan gidan sa da sanyin safiya.
Duk da Amurka ce ta fara bayyanawa duniya kisan da tayi masa hukumomi a Tehran basu kai ga fidda sanarawar ba har sai ranar 1 ga Maris, kwana guda a tsakani.
Marigayi Ali Khamenei ya shafe shekaru 37 yana mulki a matsayin Jagoran Juyin Juya Hali, bayan ya karbar jagorancin a Shekarar 1989, bayan binne Ayatollah Ruhollah Khomeini a ranar 6 ga watan Yuni, na shekarar.
Mahukuntan Iran sun ce suna sa ran mutane miliyan 20 za su halarci bikin juyayin daga lunguna da sakunan kasar. An ayyana lokacin makoki na kasa don gudanar da bukukuwan.
Za a yi jerin gwanon jana’izar Khamenei a akalla manyan birane uku: Tehran, Qom, da Mashhad. Ana sa ran kowane jerin gwano zai dauki akalla awanni 24, bisa wasiyyar Khamenei.
