Yayin da dambarwar ganin jinjirin watan Shawwal ta karu a tsakanin al’umma, fitaccen masanin nan na ilimin falaki, Nasiru Alfalaky Alkanawy, ya fito da bayanan da suka nuna dalilin da ya sa dole azumin Ramadan na wannan shekara ta 1447 bayan Hijira ya cika kwanaki talatin (30) ga wadanda suka fara a ranar 18 ga watan Fabrairu.

Shin Me Ya Faru Da Jinjirin Watan Shawwal?

A cewar Alfalaky Alkanawy, a halin yanzu da ake wannan bayanin, rana da wata suna cikin wani yanayi na sararin samaniya da ake kira Burujin Hutu.

Ya ce za a samu abin da ake kira Iqtiran (wato haifuwar jinjirin wata) ne kawai lokacin da rana da wata suka hadu a matsayi daya a Manzila daya.

Masanin ya fayyace lissafin kamar haka:

* Lokacin Haihuwar Wata: Wannan zai faru ne da misalin karfe 2:23 na dare (Agogon Najeriya).
* Matsayin Kano: A birnin Kano, tsohon watan Ramadan ya fadi ne tun karfe 5:17 na yamma, yayin da rana ba ta fadi ba sai karfe 6:37 na yamma.
* Sakamako: Wannan tazarar tana nufin cewa a lokacin duba wata bayan faduwar rana, ba a ma haifi sabon watan Shawwal ba a doron kasa.

“Ganin Watan Wata Kasa”
Nasiru Alfalaky ya jaddada cewa, matsalar ta samo asali ne tun daga ranar Talata, 18 ga Fabrairu, lokacin da wasu suka dauki azumi bisa dogaro da kalanda ko ganin watan wata kasa wanda bai yi daidai da ganin wata na shari’a ba.

“Maganar gaskiya, an yi amfani da kalandar ne ba ganin watan da Shari’a ta ce ba.

“Saboda haka, an yi zakkar azumin farko, yanzu kuma sai a cika na karshe na Shari’a,” in ji Alfalaky Alkanawy.

Duk da cewa masanin ya taba cewa ba zai sake yin magana a kan dambarwar ganin wata ba saboda yadda “son rai” ya mamaye lamarin, ya ce ya fadi wannan bayani ne saboda yawaitar kiran da ’yan uwa suke masa na neman karin haske.

Wannan bincike nasa ya nuna cewa lissafin falaki ba ya fada da Shari’a, face dai yana kara tabbatar da cewa ya zama dole a cika kwanaki talatin domin dacewa da umarnin addini.

Rahoto Daga: Blueprint Hausa Digital Team.
Bincike Da Sharhi: Nasiru Alfalaky Alkanawy.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *