Vinicius Jr ya kubutar da Brazil daga kunyar shan kaye a wasan farko na Kofin Duniya bayan kwallon da ya zura shi kadai ta.
Wannan ce bai wa waɗanda suka lashe kofin sau biyar damar canjaras da Maroko a filin wasa na New York, da ke New Jersey.
Dan wasan gaban Marokon Ismael Saibari, shi ne ya fara zura wa Brazil kwallo a raga a minti na 21 da take wasa.
Wannan ne karon farko da zakarun Afirkan suka zura kwallo a ragar wata tawaga daga Kudancin Amurka a gasar Kofin Duniya.
- Canada ta tashi canjaras da Bosnia-Herzegovina
- Dan asalin Najeriya ya jagoranci Amurka ta doke Paraguay
A wani wasan na dabam, John McGinn ya mayar da martani ga amincin da koci Steve Clarke ya nuna masa ta hanyar zura kwallo daya tilo wadda ta bai wa Scotland nasararsu ta farko a gasar, cikin shekaru 36 bayan da suka doke Haiti a dawowarsu gasar ta maza bayan rashin shiga na tsawon shekaru 28.
Kazalika, kwallaye a kowane rabin lokaci daga Nestory Irankunda da Connor Metcalfe sun sa Australia ta doke Turkiya 2-0 a wasansu na farko na Rukunin ‘D’, gasar cin Kofin Duniya a Vancouver.