Cristiano Ronaldo ya zura ƙwallaye biyu yayin da Portugal ta lallasa Uzbekistan da ci 5-0 a gasar cin kofin duniya da suka buga a ranar Talata.
Ronaldo, wanda ya zama ɗan wasa na farko da ya zura ƙwallo a gasar cin kofin duniya daban-daban har guda shida, ya fuskanci suka sosai bayan rashin tasiri a wasan farko da Portugal ta buga da DR Congo, inda suka yi kunnen doki mai ban mamaki da ci 1-1.
-
Faransa 3-0 Iraq: Mbappe ya zura ƙwallaye biyu a wasansa na 100 da Faransa
-
Argentina 2-0 Austria: Messi ya karya tarihin cin ƙwallo a gasar cin kofin duniya
A halin yanzu, adadin ƙwallayen da Ronaldo ya zura a gasar cin kofin duniya sun kai 10, kuma ya zura ƙwallaye 975 a tarihin rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
Ronaldo ɗan shekara 41, yanzu shi ne wanda ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin ƙasarsa a gasar cin kofin duniya.
