Dakarun sashi na 2 na Bataliya ta 135 ta Musamman ƙarƙashin Operation HADIN KAI sun yi nasarar tarwatsa shingen hanya da ‘yan ta’addan ISWAP suka kafa a hanyar Buratai zuwa Kamuya, a Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno, inda suka ceto fararen hula 53 tare da kwato motoci 8.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 24 ga Yuni, 2026, lokacin da dakarun da ke Dutse Kura suka hango ‘yan ta’adda suna tare hanya ta amfani da kyamarorin sa ido.
Cikin wata sanarwa da mukaddashin kakakinrundunar kyaftin Muhammad Goni ya fitar, yace nan take aka tura Rundunar Gaggawa (QRF) zuwa wurin, inda suka bi sahun ‘yan ta’addan har zuwa yankin Mangari–Dora suka yi musayar wuta da su, lamarin da ya tilasta musu guduwa.
- CBN ta umarci bankuna su daskarar da asusun mutanen da ake zargi da ɗaukar nauyin ta’addanci
- Zaben 2027: PDP ta baiwa Pantami Takardar shaidar takarar gwamnan Gombe
- Ba mu kai ‘yan bindiga aikin Hajji ba – Gwamnatin Katsina
Bayan artabun, dakarun sun ceto mutane 53 da kuma kwato motoci 8 da ‘yan ta’addan suka sace.
Daga bisani dakarun sun gudanar da sintiri a yankin, sannan aka kai wadanda aka ceto da kayan da aka kwato zuwa Buratai don kula da su.
Rundunar ta yaba da saurin daukar mataki da kwarewar dakarun, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanan tsaro domin taimakawa yaki da ta’addanci.