Ana ci gaba da samun ƙarin goyon baya kan ƙudirin kafa ’yan sandan jihohi a Nijeriya bayan da Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai bai wa jihohi damar kafa nasu tsarin ’yan sanda domin tinkarar matsalolin tsaro da suka addabi sassa daban-daban na ƙasar.
Cikin masu nuna goyon baya akwai gwamnoni, kakakin majalisun dokokin jihohi 36, Jam’iyyar LP da kuma ƙungiyar kakakin majalisun dokokin jihohin da ke ƙarƙashin Jam’iyyar APC. Sun bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen magance matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane, rikice-rikicen al’umma da kuma sauran matsalolin tsaro da suka yi kamari a ƙasar.
Sai dai kudirin na buƙatar samun amincewar aƙalla majalisun dokokin jihohi 24 kafin a aika wa Bola Ahmed Tinubu domin rattaba hannu.
- Ƙudirin kafa ƴan sandan jihohi ya samu sabon ci gaba, bayan da Majalisar Dattawa ta amince da shi.
- Gwamnatin Tarayya ta gano tarin ma’adanai masu daraja a Jihar Kaduna
- Majalisar Tarayya ta sake tsawaita aiwatar da kasafin 2025 zuwa Satumba
Masu goyon bayan ƙudirin na ganin cewa tsarin ’yan sanda na jihohi zai ba kowace jiha damar samar da jami’an da suka fi fahimtar yankunansu da al’adu da matsalolin da al’ummarsu ke fuskanta.
Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia ne, ya bayyana kudirin a matsayin wani babban mataki na ƙarfafa tsarin tsaro, yayin da wasu jihohi kamar Kano da Gombe da Bayelsa da Filato suka fara nazari domin bayyana matsayinsu.
Sai dai duk da wannan goyon baya, Jam’iyyar PRP ta nuna adawa da ƙudirin, inda ta yi zargin cewa gwamnatin APC ba ta da cikakken amincewar jama’a da za ta jagoranci irin wannan babban sauyi a tsarin tsaro.
Shugaban jam’iyyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce akwai buƙatar a dakatar da batun har sai bayan babban zaɓe na gaba, yana mai cewa akwai fargabar amfani da rundunar wajen murƙushe masu adawa da gwamnati.
Duk da irin wannan fargaba, ƙudirin ya tanadi wasu matakan kariya domin hana gwamnoni amfani da rundunar domin biyan buƙatun siyasa.
Ƙudirin ya haramta wa gwamnoni bai wa kwamishinonin ’yan sanda umarnin kama ko binciken wani mutum ko ƙungiya ba bisa doka ba, sannan gwamnatin tarayya za ta iya shiga idan aka samu take haƙƙin jama’a ko barazanar tsaron ƙasa.
Haka kuma an faɗaɗa majalisar kula da harkokin ’yan sanda ta ƙasa wadda ta haɗa da lauyoyi, ƙungiyar ƙwadago da masu rajin kare haƙƙin bil’adama.
A taƙaice, muhawarar kafa ’yan sandan jihohi na nuna cewa Nijeriya na neman sabuwar hanyar tinkarar matsalolin tsaro da suka daɗe suna addabar ƙasar.