Minsitan yace gyara tsarin haraji zai taimakawa bunƙasar ci gaban ƙasa.

Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce babban ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta a bangaren tara kudaden shiga shi ne ƙarancin masu biyan haraji, ba wai yawan kuɗin harajin da ake karɓa ba.

Oyedele ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake karɓar shugabannin Cibiyar Kwararrun Masana Harkokin Haraji ta Nijeriya bayan kammala bikin ranar wayar da kan jama’a kan haraji na farko da cibiyar ta shirya.

Ya ce ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana inganta tsarin biyan haraji a ƙasar shi ne yadda mutane da dama ke kallon cewa duk lokacin da gwamnati ta yi magana kan haraji, tana neman ƙarin kuɗi ne kawai daga hannun jama’a.

A cewar sa, Najeriya har yanzu ba ta samun isassun kuɗaɗen shiga daga haraji, yana mai jaddada cewa abin da gwamnati ke nema shi ne tabbatar da cewa duk wanda ya kamata ya biya haraji ya yi hakan, domin samar da adalci a tsarin tara kuɗaɗen shiga.

Ministan ya ƙara da cewa idan aka gyara tsarin haraji yadda ya kamata, hakan zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa ci gaban ƙasa.

Ya kuma buƙaci cibiyar ta samar da lambobin yabo na shekara-shekara domin karrama mutanen da suka fi bin doka wajen biyan haraji, a matsayin wata hanya ta ƙarfafa wa mutane gwiwar riƙa biyan haraji da kansu.

Wannan na zuwa ne shekara guda bayan Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu kan dokokin gyaran tsarin haraji na Nijeriya a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 2025, wani mataki da gwamnati ke ganin zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin ƙasa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *