Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Abdulrazak Sa’ad Namdas a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar Raya Al’ummomin Kan Iyaka (Border Communities Development Agency – BCDA).

Gidan Rediyon VON ya ruwaito cewa Namdas ya maye gurbin Dakta Dakorinama Alabo George, wanda ya yi murabus domin tsayawa takarar mukamin siyasa a jihar sa.

Haka kuma, Shugaban ƙasa ya naɗa Hon. Patrick Obahiagbon a matsayin Darakta Zartarwa mai kula da Tsare-tsare da Kasuwanci a Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Neja Delta (Niger Delta Power Holding Company – NDPHC).

Obahiagbon ya maye gurbin Injiniya Omoregie Ogbeide-Ihama, wanda shi ma ya yi murabus domin tsunduma harkokin siyasa.

Tinubu ya kuma sake naɗa Mr. Chukwuma Umeoji a matsayin Darakta Zartarwa mai kula da Harkokin Gudanarwa (Corporate Services) na hukumar NDPHC.

Dukkan waɗannan naɗenaɗen dai sun fara aiki nan take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *