Manyan kafofin yaɗa labarai na Ƙasar Uganda sun bayyana cewa suna fuskantar “mamayar sojoji” bayan hafsan rundunar sojin ƙasar ya ba da umarnin rufe gidajen talabijin, rediyo da jaridu.
An tilasta wa tashoshin NTV Uganda da Spark TV dakatar da shirye-shiryensu bayan wasu sojoji dauke da makamai sun kewaye hedikwatar Nation Media Group (NMG) da ke Kampala a ranar Lahadi
Matakin ya biyo bayan sanarwar da Hafsan sojin Uganda, Janar Muhoozi Kainerugaba, ya wallafa a shafinsa na X, cewar kafafen yaɗa labaran za su dakatar da ayyukansu nan take.
- DR Congo za ta ƙara da Ingila a zagayen ƙasashe 32 bayan ta doke Uzbekistan
- Israila da Lebanon sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta
- Kenya ta tsaurara tsaro yayin da aka cika shekaru biyu da zanga-zangar matasan Gen Z
Janar Kainerugaba, wanda ɗan Shugaba Yoweri Museveni ne, ya ƙara nuna ƙarfinsa a watannin baya-bayan nan, inda ya ba da umarnin kama wasu ‘yan siyasa da masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam.
Ya kuma tabbatar a shafin sa na X cewa mahaifinsa, Shugaba Yoweri Museveni, ya amince da matakin, yana mai cewa kafafen yaɗa labaran “ba za su koma bakin aiki ba sai da izinina.”
Museveni mai shekaru 81 ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a watan Janairu, amma da dama na ganin ɗansa na ƙoƙarin gadon sa a shugabancin ƙasar bayan kusan shekaru 40 da Museveni ya shafe yana mulki
Tashoshin sun daina watsa shirye-shirye tun da sanyin safiyar Lahadi 28/6/2026, inda wasu kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka ruwaito cewa masu kallo sun riƙa ganin saƙon ba’a samun bidiyon “Video unavailable”.
Kamfanin Nation Media Group, wanda hedikwatarsa ke ƙasar Kenya, shi ne mafi girman kamfanin yaɗa labarai mai zaman kansa a Gabashin Afirka.
A Uganda, kamfanin ne ke mallakar jaridun Daily Monitor da The East African da wasu kafafen yaɗa labarai masu tasiri.
Kwamitin Kare ‘Yan Jarida (Committee to Protect Journalists) da jagoran jam’iyyar adawa, Bobi Wine, sun yi Allah-wadai da rufe kafafen yaɗa labaran
A cewar ƙungiyar Reporters Without Borders, Uganda tana matsayi na 143 cikin ƙasashe 180 a ma’aunin ‘yancin aikin jarida na duniya.
Ƙungiyar ta ce ‘yan jarida a Uganda na fuskantar barazana da cin zarafi kusan a kowace rana.