Rundunar Operation HADIN KAI (OPHK), tace wasu manyan shugabannin ƙungiyar ISWAP sun fice daga maboyarsu tare da miƙa wuya ga dakarun soji sakamakon matsin lambar da suke ci gaba da fuskanta.

A Sanarwar da jami’in yaɗa labarai na rundunar Kyaftin Mohammed Goni ya fitar, ta ce waɗanda suka miƙa wuya suna hannun hukumomin soji a wani wuri mai tsaro, inda ake gudanar da tantancewa, yi musu tambayoyi da kuma sauran matakan da dokokin aikin soji suka tanada.

Rundunar ta bayyana cewa ci gaba da hare-haren da ake kai wa ‘yan ta’addan ya haifar da rushe sansanoninsu, lalata hanyoyin sadarwa da samar musu da kayan aiki, tare da hana su damar gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Gabas.

A cewar sanarwar, hare-haren sun kuma rage ƙarfin mayaƙan ƙungiyoyin tare da raunana kwarin gwiwar shugabanni da mabiyansu.

Mohammed ya ƙara da cewa cikin mako guda da ya gabata, mayaƙan ‘yan ta’adda 76, tare da wasu daga cikin iyalansu, sun miƙa wuya ga dakarun soja.

Rundunar ta ce waɗannan nasarori sun nuna tasirin dabarun yaƙi da ta’addanci da rundunar sojin Najeriya ke amfani da su, waɗanda suka haɗa da kai hare-hare cikin tsari, amfani da bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da matsa wa ragowar ‘yan ta’adda lamba har sai an murƙushe su gaba ɗaya ko kuma sun miƙa wuya, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *