'Yan wasan Moroko suna murna bayan samun nasara aka Holand

Yassine Bounou ya zama jarumi ga Morocco yayin da suka doke Holand da ci 3-2 a bugun fenariti a zagaye na 32 na Gasar Cin Kofin Duniya, bayan wasan ya ƙare 1-1 bayan ƙarin lokaci.

Mai tsaron ragar Moroko ya tseratar da bugun dag Crysencio Summerville kafin Ismael Saibari ya ci bugun fenaritin karshe da ya tabbatar da nasarar Moroko.

A wasan gaba Moroko za ta fafata ne da Canada a zagaye na 16.

Da farko dai, Issa Diop ne ya ci ƙwallon da Moroko ta farke a minti na 91 don dai-daita ƙwallon farko ta Cody Gakpo ga Holand.

Yanzu haka, an fitar daƙasar Holand a bugun fanareti a gasanni biyu a jere na Kofin Duniya.

Inda Moroko ta ci bugun fanareti biyu a Gasar Cin Kofin Duniya, bayan ta taɓa doke Spaniya a zagaye na 16 a 2022, kuma ba tare da shakka ba za su samu ƙwarin guiwa wajen fuskantar Canada a zagaye na 16.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *