Gwamnatin Jihar Cross River ta yi wa gidan ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar PDP na zaɓen 2027, Alphonsus Eba, da wasu gidaje kusan 20 alamar rusau.
Hukumar Tsara Birane ta jihar, ta bayyana cewa an gina gidajen ne ba bisa ƙa’ida ba a yankin da aka tanada domin bututun Hukumar Samar da Ruwa ta jihar, lamarin da ke barazana ga lafiyar jama’a da muhimman kayayyakin gwamnati.
Hukumar ta ce ci gaba da zama ko gine-gine a yankin na iya hana gyara da kula da bututun ruwa, tare da ƙara haɗarin fashewar bututun da gurɓata ruwan sha.
- Tinubu ya amince da ayyukan tituna 27 na Naira tiriliyan 3.9 a jihohi 15
-
Zaben 2027: PDP ta baiwa Pantami Takardar shaidar takarar gwamnan Gombe
Sai dai Eba ya yi watsi da matakin gwamnatin, yana mai zargin cewa siyasa ce ta haddasa shi. Ya ce ko da an rusa gidansa ko aka kashe shi, hakan ba zai yi wani tasiri ga makomar siyasar sa ba.
Ya kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Cross River, Bassey Otu, da kada ya wuce gona da iri wajen tafiyar da harkokin siyasa, yana mai cewa neman takara ba laifi ba ne.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Erasmus Ekpang, ya ce rushe gidajen ba shi da alaƙa da siyasa, yana mai bayyana cewa gidajen da abin ya shafa sun haɗa har da na wasu jami’an gwamnatin jihar.
Ya kuma buƙaci ‘yan siyasa su daina haɗa ayyukan ci gaba da batun siyasa.
