Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya aika da kakkausan saƙo ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu game da taɓarɓarewar tsaro a wasu sassan ƙasar nan.
Atiku ya ce alƙawuran da Shugaban Ƙasar yake yi cewa hare-hare ba za su sake faruwa ba sun zama “kalaman baki”.
- ‘Tinubu zai gana da Mutfwang kan hare-haren Jos’
- Matsalar Arewa za ta shafi Najeriya –Zainab Buba Galadima
Atiku ya kuma tunatar da Tinubu game da kalamansa na baya-bayan nan a kan harin Angwan Rukuba, inda Shugaban ya tabbatar da cewa hakan ba zai sake faruwa ba.
Sai dai ba a wuce sa’o’i 72 da yin wannan furuci ba aka sake kai wani harin a Jihar Binuwai, wanda ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane sama da 12.
Atiku ya nuna damuwarsa matuƙa kan halin da ake ciki a jihohin Nasarawa da Kaduna, inda iyalai da dama suka tsere domin neman mafaka, yayin da ake sabunta hare-haren a wasu yankuna.
“Waɗannan kalaman na baki sun isa haka, lokaci ya yi da za ka naɗe hannun riga ka fuskanci aikin dake gabanka,” inji Atiku.
Atiku ya kuma miƙa saƙon ta’aziyya da addu’o’i ga dukkan iyalai da suka rasa ‘yan uwansu a waɗannan hare-hare da suka faru.
Don samun ƙarin labarai, ku ci gaba da kasancewa da Blueprint Radio.