Gwamnati ta umarci kamfanin Meta da ya dakatar da ƙaddamar da sabon fasalin suna (Username) a manhajar WhatsApp, tare da neman cikakken bayani daga kamfanin cikin kwanaki uku.

Ma’aikatar fasahar sadarwa da bayanai ta Indiya ta bayyana cewa sabon tsarin na iya bai wa masu aikata laifukan yanar gizo damar kirkirar sunaye masu kama da na wasu mutane ko hukumomi domin yaudarar masu amfani, musamman waɗanda ba su da cikakken ilimin fasahar zamani.

WhatsApp ta sanar a baya cewa sabon fasalin zai bai wa masu amfani damar tattaunawa ta hanyar sunan mai amfani maimakon bayyana lambar waya, domin ƙara kare sirrin masu amfani.

Sai dai gwamnatin Indiya, wadda ke da sama da masu amfani da WhatsApp miliyan 500, ta ce ta nemi Meta da ta dakatar da fara amfani da wannan fasali a ƙasar har sai an kammala tattaunawa kan matakan kariya daga damfara.

A nata ɓangaren , Meta ta ce har yanzu ba a fara amfani da fasalin a Indiya ba, kuma ta riga ta tanadi sunayen fitattun mutane da kuma asusun da aka tabbatar da ingancinsu domin hana masu damfara yin amfani da su.

Kamfanin ya kuma jaddada cewa duk da amfani da sunan mai amfani, har yanzu ana buƙatar lambar waya domin buɗe asusun WhatsApp, tare da cewa an gina ƙarin matakan tsaro don dakile damfara da satar bayanai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *