Ministan Matasa, Ayodele Olawande ya yi martani game da bayanan da ake dangantawa dashi na sauyawa masu bautar kasa kaki.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis 3 ga watan Yuli, Ministan ya ambaci Adire da Ankara ne kawai a matsayin misalin wasu daga cikin shawarwarin da ya gabatar wa gwamnati.
Ayodele yace kawo yanzu, gwamnatin tarayya ba ta yanke hukunci akan wanan batu kamar yadda ake ta yamadidi ba.
Ya bayyana cewa gwamnati na nazarin shawarwari game tsarin da zai dace da kasarnan, ta fuskar ɗorewa, sauƙin amfani, da ƙarancin tsada da kuma fito da martabar ƙasar a idon duniya.
- Gwamnatin Tinubu ta yi Sabon sauye sauye a fannin kiwon lafiya tare da faɗaɗa ayyukan a Najeriya
- ‘Yan Sanda sun daƙile yunƙurin barazanar tsaro a harabar Cibiyar NIPSS
- EFCCn neman Olusegun Ola Osinkolu ruwa a jallo
Ministan ya buƙaci ‘yan Najeriya su mayar da hankali kan manyan sauye-sauyen da ake shirin yi wa hukumar kula da masu bautar kasa (NYSC), da suka haɗa da inganta damar samun aikin yi, bunƙasa kasuwanci.
An kirkiri hukumar ta (NYSC) a shekarar 1976 zamanin gwamnatin mulkin soja, ta Janar Yakubu Gowon.
Sai dai tunda aka kafa ta, babu wasu sauye-sauye masu daukar hankali da aka shirya yi mata kamar irin na wannan lokaci, da ya haifar da cece-kuce daga ciki da wajen kasar.