Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya na ci gaba da kasancewa muhimmin ginshiƙi na manufofin gwamnatinsa na ‘Renewed Hope Agenda’.
Shugaban ya ce an ƙirƙiri shirin ne domin rage giɓin mitocin wutar lantarki a ƙasar da kawo ƙarshen tsarin cajin kuɗin wuta na ƙiyasta kare haƙƙin masu amfani da wutar lantarki tare da ƙarfafa tsarin kasuwar lantarki a Najeriya.
A cewarsa, shirin ba wai kawai zai samar da ayyukan yi ba ne, har ma zai bai wa matasa ƙwarewar sana’a da za ta haɗa su da damar aiki a wani muhimmin fanni da ya shafi gidaje da kasuwanci da al’ummomi a faɗin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa damar shiga shirin zai kasance ga ‘yan Najeriya da suka kammala karatun sakandare, yayin da aka tanadi kaso na musamman ga masu yi wa ƙasa hidima a ƙarƙashin shirin NYSC.
- Blueprint Radio ta ziyarci Jaridar Blueprint Abuja
-
‘Yan Sanda sun daƙile yunƙurin barazanar tsaro a harabar Cibiyar NIPSS
Ya ƙara da cewa samar da mitoci ga gidaje da wuraren kasuwanci zai taimaka wajen tabbatar da cewa masu amfani da wutar lantarki suna biyan kuɗin abin da suka amfani da shi kawai.
Haka kuma, zai inganta gaskiya wajen tattara kuɗaɗen shiga ga kamfanonin rarraba wutar lantarki, wanda zai ba su damar rage asar da kula da kayayyakin more rayuw da faɗaɗa hanyoyin samar da wuta da kuma inganta ayyukansu.
Tinubu ya ce wannan mataki zai taimaka wajen gina ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki wanda zai kasance mai adalci ga masu amfani da ƙarfafa masu zuba jari tare da samar da ingantacciyar wutar lantarki ga ‘yan Najeriya.
Ya kuma buƙaci matasan da suka cancanta da su nemi shiga shirin ta hanyar yin rajista a shafin pmi.naptin.gov.ng.