Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci kafafen yaɗa labarai a Najeriya da su fifita sahihan bayanai maimakon neman jan hankali, yana mai gargadin cewa yaɗa labaran ƙarya da bayanan da ba a tantance ba na iya jefa ƙasa cikin matsala.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a taron cin abincin dare na farko da ya haɗa shi da wakilan kafafen yaɗa labarai masu bibiyar harkokin Fadar Shugaban Ƙasa da aka gudanar a Abuja.
Ya ce duk da cewa ‘yancin faɗar albarkacin baki da na aikin jarida su ne ginshiƙan dimokuraɗiyya, dole ne a haɗa wannan ‘yanci da ɗaukar nauyin tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa.
- Ministan Matasan Najeriya ya magantu sauyawa masu bautar kasa kaya zuwa Kamfala
- Gwamnatin Tarayya za ta horas da matasa 5,000 kan gyaran mitocin wutar lantarki
Shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda labaran ƙarya, da bayanan yaudara, da fasahohin ƙirƙirar sauti da hotuna na bogi ke ƙaruwa, yana mai cewa bai kamata ƙwararrun ‘yan jarida su zama hanyar yaɗa bayanan da ba a tantance ba.
Ya ƙara da cewa kafafen yaɗa labarai su zaɓi gaskiya maimakon ƙarya, su fifita ingantattun rahotanni maimakon neman masu kallo ko masu bibiya ta hanyar labaran da ke tayar da hankali.