Shugabar ƙungiyar mata ta Peace Revival and Reconciliation Foundation of Nigeria, Hajiya Ramatu Tijjani, ta raba rigunan tsaron ruwa (life jackets) ga masu ceto a Kogin Kaduna domin rage yawan mace-macen da ke faruwa sakamakon nutsewa a lokacin damina.

An gudanar da rabon ne a bakin Kogin Kaduna, da nufin ƙara kare lafiyar masu ceto waɗanda ke sadaukar da rayuwarsu wajen ceto mutanen da ke cikin haɗarin nutsewa.

 Hajiya Ramatu Tijjani ta ce masu nutsu don ceto waɗanda suka nutse a ruwa na taka muhimmiyar rawa a lokacin ambaliya da sauran haɗurran da suka shafi ruwa.

Ramatu Tijjani kuma bayyana cewa waɗannan masu ceton sun taimaka wajen ceto mutanen da suka yi yunƙurin kashe kansu sakamakon matsin rayuwa da kuma matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa.

Ta ce irin wannan gudunmawa da suke bayarwa ta cancanci a karrama su a matakin ƙasa saboda irin muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ceton rayukan jama’a.

Hajiya Ramatu ta yi kira ga masu hannu da shuni da sauran masu ruwa da tsaki da su tallafa wa masu ceton da ƙarin rigunan tsaron ruwa da sauran kayan aikin ceto domin su sami damar ceton rayuka da dama a lokacin ambaliya da sauran bala’o’in da suka shafi ruwa.

Ta kuma bayyana cewa nan gaba za ta kai irin waɗannan rigunan tsaron ruwa ga masu ceton da ke Zariya domin su ma su ci gaba da ceton rayukan jama’a.

Da yake jawabi a madadin masu ceton, Mallam Dattijo Gada na Kaduna ya gode wa Hajiya Ramatu Tijjani bisa wannan tallafi, tare da yi mata addu’ar Allah Ya saka mata da alheri.

Jakadiya Ramatu Tijjani ce ta jagoranci rabon kayan a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan ceto da tallafa wa al’ummomin da ke zaune a kusa da koguna.

Ana sa ran wannan shiri zai taimaka wajen rage mace-macen da ke da alaƙa da ruwa, tare da inganta ayyukan ceto musamman a lokacin da damina ke ƙarfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *