Mutumin da ke iƙirarin cewa shi ne Darakta Janar na ƙungiyar da ake kira Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), Adeniyi Adeyemi, ya bayyana cewa a shirye yake ya fuskanci shari’a domin wanke sunansa.

Adeyemi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce kotu ce kaɗai za ta tantance gaskiya kan zarge-zargen da ake masa.

Ya ce, “Idan na yi kuskure, kotu ta yanke hukunci a kaina. Idan kuma ina da gaskiya, kotu za ta tabbatar da hakan. A shirye nake in kare kaina tare da wanke sunana.”

Adeyemi ya musanta zargin cewa ɗan damfara ne, yana mai cewa tun da batun yana gaban kotu, bai dace ya yi ƙarin bayani ba.

Ya ƙara da cewa lauyoyinsa sun riga sun shiga cikin lamarin, kuma zai bar kotu ta gudanar da aikinta.

Da aka tambaye shi inda kuɗin biyan ma’aikatan ƙungiyar suka fito, Adeyemi ya ƙi yin bayani, yana cewa gaskiyar lamarin za ta fito ne a kotu.

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta nesanta kanta da ƙungiyar PFIPC, tana mai cewa babu wata hukuma mai irin wannan suna a ƙarƙashin gwamnatin tarayya.

Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya zargi Adeyemi da kwaikwayon jami’in gwamnati da kuma amfani da takardun bogi. A cewarsa, Adeyemi ya yaudari wasu jami’an gwamnati da jama’a ta hanyar ikirarin cewa yana jagorantar wata hukuma da ba ta wanzu ba.

A nasa ɓangaren, Adeyemi ya musanta dukkan zarge-zargen, tare da yin iƙirarin cewa wasu manyan jami’an gwamnati, ciki har da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, suna ƙoƙarin dakile ayyukansa.

Ya kuma yi zargin cewa an nemi wani kaso na kuɗin tallafin fara aikin hukumar daga gare shi, zargin da babu wata hujja da ta tabbatar da shi, kuma waɗanda ake zargin sun musanta.

Adeyemi ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciken dukkan zarge-zargen da ake yi.

A halin yanzu dai, batun yana gaban kotu, inda ake sa ran shari’ar za ta fayyace gaskiyar lamarin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *