Gwamnatin Jihar Kogi tare da haɗin gwiwar Briged ta 12 ta Rundunar Sojin Najeriya, sun samu nasarar kwato kimanin dabbobi 1,000 da aka sace.

Wannan dai na daga cikin farmakin da ake kai wa ragowar ƙungiyar ‘yan bindiga ta Kachalla Ibrahim Battijo, da kuma sauran ƙungiyoyin masu satar shanu a Jihar Kogi da yankin Arewa ta Tsakiya.

An dai kai farmakinne tare da haɗin gwiwar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da masu aikin sa-kai da mafarauta.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar, Gwamnatin ta ce daga cikin dabbobin da aka ƙwato, sama da 200 na da alaƙa da ragowar ƙungiyar Battijo, yayin da sauran da aka ƙwato daga wasu ƙungiyoyin masu garkuwa da dabbobi da ke aiki a Kogi da jihohin maƙwabta.

Ya ce bayan samun bayanan sirri, jami’an tsaro sun yi artabu da ‘yan bindigar a wurare daban-daban, inda aka kashe da dama daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga, suka bar dabbobin domin tsira da rayukansu. Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da farautar waɗanda suka tsere.

A cewarsa, ragowar ƙungiyar Battijo sun shiga cikin matsanancin hali tun bayan kashe jagoransu, sakamakon hare-haren da jami’an tsaro ke ci gaba da kai musu tare da lalata hanyoyin gudanar da ayyukansu da samar musu da kayan aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *