Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na yin haɗin gwiwa da shugabannin addinai domin inganta zaman lafiya da haƙuri da kuma tattaunawar addinai daban-daban a tsakanin al’ummomin Najeriya masu bambancin addini da al’adu.
Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da ya karɓi Archbishop Paul R. Gallagher, Sakataren Hulɗa da Ƙasashe da Ƙungiyoyin Ƙasa da Ƙasa na Holy See.
Shafin Muryar Najeriya (VON), ya ruwaito shugaban na cewa tattaunawa tsakanin mabiya addinai na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tsaro, tare da yabawa Cocin Katolika bisa gudummawar da take bayarwa a fannonin ilimi da kiwon lafiya da ayyukan jin ƙai da kuma inganta zaman lafiya a faɗin duniya.
- Sojoji sun kashe mutane shida da ake zargin ’Yan ta’adda ne a Filato
- “Hukumar bogi”: Atiku ya buƙaci Tinubu ya binciki badaƙalar
- Oluremi Tinubu ta bai wa ɗakunan karatu na makaranatun Gwamnati littattafai 140, 000
Shugaban ya ce gwamnatinsa na aiki don kare ‘yancin kowane mutum na gudanar da addininsa, ci gaba da bunƙasa nasarorin da aka samu a harkar tsaro da ƙarfafa sa ido a yankunan da ke da barazana da kuma zuba jari a matasa domin rage yiwuwar faɗawarsu cikin tsattsauran ra’ayi da kuma amfani da su wajen ayyukan ta’addanci.
A nasa jawabin, Archbishop Gallagher ya ce ziyararsa ta zo ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 50 da ƙulla dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Holy See.
Ya bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai matuƙar muhimmanci ga nahiyar Afirka, tare da yabawa Shugaba Tinubu kan ƙoƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya, inganta tsaro da kuma goyon bayan da yake bai wa Cocin Katolika.
Ziyarar dai na zuwane ƙasa da mako guda da Ƙasar Amurka ta ce ta kawo ƙarshen kisan kiristoci a Najeriya, lamarin da yasa ta janye sojinta daga kasar.