Dalibai a wasu makarantun dake kewayen Birnin Abuja na ci gaba da zama a ƙasa, tare da yin karatu a ƙarƙashin bishiyoyi ko rumfunan wucin gadi saboda ƙarancin gine-ginen azuzuwa da kayan more ilimi, lamarin da ke jefa makomar karatunsu cikin ƙalubale.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Ɗaya daga cikin waɗannan ɗalibai shi ne Badiku Saliu mai shekara tara, ɗalibi a Makarantar Firamare ta LEA Nomadic da ke Yangoji ta yamma a wajen Birnin Tarayya Abuja.

Yaron kan zauna a kan tsohon buhun roba a ƙarƙashin rumfar da aka yi da ganyen dabino da turaku, yana rubutu tare da kallon allo da littafinsa yayin da malaminsa ke koyar da darasin lissafi.

 

 

Duk da cewa hasken rana na ratsawa ta ramukan rumfar, Saliu na ci gaba da mai da hankali kan darasi.

Ya ce ya shafe fiye da shekara huɗu yana karatu a irin wannan yanayi, inda suke halartar darussa ba tare da zama a rumfa ba, a lokutan ruwan sama da kuma tsananin zafi.

Rahoton ya nuna cewa irin wannan yanayi na ci gaba da addabar wasu makarantun yankunan dake kewaye da babban birnin tarayya Abuja.

Masharhanta na cewa akwai buƙatar hukumomi da masu ruwa da tsaki su samar da ingantattun azuzuwa da kayan koyo da koyarwa, domin bai wa yara damar yin karatu cikin yanayin da ya dace.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *