Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris, ya buƙaci ‘yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta a Arewacin Najeriya su dinga tantance irin labarai da suke wallafawa game da yankin.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake gabatar da jawabi a taron masu ruwa da tsaki na Arewa Media Summit da aka gudanar a birnin Kano.
A cewarsa, ci gaban Arewacin Najeriya ba zai dogara ga manyan ayyukan gine-gine, noma ko masana’antu kaɗai ba, har ma da irin labaran da ake yaɗawa game da yankin.
- ‘Yan Sanda sun kashe ɗan Bindiga a Sakkwato
- Najeriya da Guinea-Bissau zasu haɗa gwiwa don bunƙasa tsaro a Yammacin Afirka
- NiMet ta yi gargaɗin ambaliya a wasu Jihohin Najeriya
Ya ce kafafen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen gina ra’ayin jama’a, jawo masu zuba jari, kare al’adu, ƙarfafa dimokuraɗiyya da bunƙasa haɗin kan ƙasa.
Ministan ya kuma yi gargaɗin cewa duk da ci gaban fasahar zamani da ya sauƙaƙa sadarwa da bunƙasar tattalin arziki, hakan ya ƙara yawan yaɗuwar bayanan ƙarya dake ruɗar da jama’a.
“A yau ƙarya na yaɗuwa cikin sauri fiye da gaskiya, sabo da haka, ƙwarewar aikin aka fi bukata, kuma dole ne ‘yan jarida su ci gaba da tabbatar da sahihancin bayanai, adalci.” in ji Ministan
Mohammed Idris ya sake jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da kare ‘yancin aikin jarida tare da samar da yanayin da zai bai wa ‘yan jarida damar gudanar da aikinsu ba tare da tsangwama ba.
Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai su daina mayar da hankali kan matsalolin tsaro kawai a Arewa, su kuma riƙa ba da haske kan nasarori da ci gaban da ake samu wajen yaki da ta’addanci
Taron na Arewa Media Summit ya samu halartar gwamnoni, ministoci, shugabannin ƙungiyoyin ‘yan jarida, masu shirya fina-finai, masana, da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban.