Hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta ta ware kimanin naira biliyan 8 da miliyan 400 a kasafin kuɗin shekarar 2026 domin gina tituna.
Bayanan kasafin kuɗin sun nuna cewa an ware wa hukumar jimillar Naira biliyan 22 da miliyan 820, a kasafin kudin bana.
Kuma an tanadi sama da Naira Biliyan 21 domin ayyukan raya ƙasa, yayin da fiye da Naira Biliyan ɗaya aka ware domin gudanar da harkokin yau da kullum.
- Ƴan siyasa na zargin Najeriya kan ikirarin IMF na kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba
- Rashin kyakkyawan yanayin karatu a wajen Abuja
- Gasar Cin Kofin Duniya: Messi, Mbappe, Kane ko Haaland, wa zai lashe Takalmin Zinare
Daga cikin manyan ayyukan da aka ware wa kuɗi akwai gina tituna a Jihar Ogun da kuma hanyoyin cikin gari a wasu yankunan Jihar Katsina da kuma hanyoyin cikin Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke garin Iyin a Jihar Ekiti.
Sannan an ware Miliyoyin Nairori domin samar da motocin ɗaukar marasa lafiya da kayan aikin cibiyar kula da haƙori da fitilun hasken rana da kuma kayan tallafa wa mata da matasa a wasu sassan Jihar Katsina.
Sai dai masana da masu fafutukar tabbatar da gaskiya a harkokin kasafin kuɗi na bayyana damuwar su, kan ayyukan da aka ware wa hukumar da cewa ba sa cikin nauyin da doka ta ɗora mata.
Hukumar wadda aka kafa a watan Mayun a shekarar 2023 ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, an ba ta alhakin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, haɗa ilimin boko da na addini da kuma inganta koyar da sana’o’i ga almajirai.