Wasu fitattun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa da suka daɗe suna wakiltar ƙasashensu sun kammala wasansu na ƙarshe a Gasar Kofin Duniya ta 2026, bayan ƙasashensu sun fice daga gasar.
Cikin ‘yan wasan akwai Cristiano Ronaldo na Portugal da Neymar na Brazil da Riyad Mahrez na Aljeriya da Guillermo Ochoa na Mexico da Manuel Neuer na Jamus.
Ronaldo ya bayyana tun kafin wasan Portugal da Spain cewa wannan ne Kofin Duniya na ƙarshe da zai buga.
Portugal ta fice ne bayan ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Spain a zagayen ‘yan 16.
- UEFA ta zargi FIFA kan haramcin janye dakatar da Balogun
- Alkalin wasan da ya baiwa Balogun Jan kati abin tuhuma ne- Trump
- Neymar ya sanar da yin murabus daga Brazil
Shi ma Neymar ya tabbatar bayan an fitar da Brazil daga gasar cewa ya kawo ƙarshen taka leda a matakin ƙasa da ƙasa, yayin da Mahrez ya sanar da yin ritaya daga tawagar Aljeriya bayan sun sha kashi a hannun Switzerland.
Haka kuma Guillermo Ochoa ya nuna alamun yin ritaya daga ƙungiyar ƙasarsa bayan ficewar Mexico, yayin da Manuel Neuer ya ce bai yi nadamar komawarsa tawagar Jamus ba duk da ficewarsu daga gasar.
Sai dai wasu fitattun ‘yan wasa irin su Lionel Messi na Argentina da Luka Modric na Croatia ba su sanar da yin ritaya ba, duk da cewa ana hasashen Gasar Kofin Duniya ta 2026 na iya kasancewa ta ƙarshe a gare su.