Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana alhinin rasuwar wata ‘yar Najeriya mai shekara 23, Nnani Adaobi Marian, wadda ta rasu sakamakon raunukan da ta samu a wani harin sama da Rasha ta kai a birnin Kharkiv na ƙasar Ukraine.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ya fitar
Sanarwar ta bayyana cewa marigayiyar ta kammala karatun aikin likita a Jami’ar Kiwon Lafiya ta Ƙasa dake Kharkiv (Kharkiv National Medical University)
- Sarkin Musulmi ya buƙaci haɗin kan addinai domin samar da zaman lafiya
- ‘Yan Arewa ba za su zaɓi Peter Obi ba – Ali Modu Sheriff
- Cibiyar nazarin dabaru NIPPS ta nemi afuwar ƙabilar Berom
Sanarwar ta kuma sake jaddada kiran da Najeriya ke yi na kai zuciya nesa game da rikicin na Ukraine, ta hanyar neman mafita cikin lumana.
Haka kuma, gwamnatin ta sake tabbatar da aniyarta na ci gaba da kare muradun da jin daɗin ‘yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen waje.
Ta ƙara da cewa za ta ci gaba da sanya ido kan yadda al’amura ke gudana tare da bayar da dukkan tallafin da ya dace ta hannun ofisoshin jakadancin Najeriya.