Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da fitar da naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari shida da biyar domin biyan kuɗaɗen tallafin karatu ga marayun jihar da ke karatu a cikin gida da ƙasashen waje.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Borno, Dokta Bala Isa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Maiduguri.

Ya ce kuɗaɗen za su biya tallafin karatu na shekarar  ta dubu biyu da ashirin da huɗu,  zuwa ta dubu biyu da ashirin da biyar, ciki har da kuɗin makaranta ga marayu dari uku na jami’an sa-kai masu taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, wato CJTF.

Haka kuma, kuɗaɗen  sun  haɗa   da biyan kuɗin makaranta da masauki ga ɗalibai  likitanci ɗari biyu da saba’in da biyu da ke Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare, da kuma kuɗin makaranta ga ɗaliban MBBS talatin da  huɗu  na Jami’ar Al-Ansar da ke Maiduguri.

Baya ga haka, za a biya kuɗin makaranta ga ɗalibai sittin na Cibiyar Nazarin Fata da Fasahar Sarrafa Fata ta Najeriya da ke Zariya, tare da alawus na watanni shida ga ɗaliban Kwalejin Koyon Aikin Jinya da ke ƙarƙashin shirin tallafin karatu na jihar.

Shirin ya kuma tanadi kuɗin tikitin dawowa gida ga ɗaliban digiri na biyu ɗari da talatin da uku da kuma ɗaliban digirin-dokta talatin da tara da ke karatu a ƙasashen Indiya da Malaysia. Haka zalika, za a biya kuɗin tikitin dawowa gida ga ɗaliban digiri na farko ɗari da huɗu da ke ƙasar Sin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *