Najeriya ta ba Jakadun tsaro na kasashe biyar izinin gudanar da ayyuka a Ƙasar

Hukumar Tattara Bayanan Asiri ta Najeriya (DIA) ta bai wa Jakadun da Wakilai a fannin Tsaro daga ƙasashen Birtaniya, Japan, Italiya, Ghana da Jamhuriyar Mali cikakken izinin gudanar da ayyukansu a Najeriya.

A wajen bikin ba su takardar izinin aiki da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, Babban Daraktan Hukumar Leken Asirin, Laftanar Janar Emmanuel Akomaye Undiandeye, ya ce wannan amincewa ce da ke ba su damar gudanar da ayyukansu a hukumance a faɗin Najeriya.

Ya jaddada muhimmancin bin dukkan matakan doka da ƙa’idoji yayin hulɗa da ma’aikatun gwamnati, hukumomi da cibiyoyin tsaro na Najeriya, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da ƙasashen su.

Emmanuel ya kuma tabbatar wa jakadun tsaron cewa za a samar musu da isasshen tsaro yayin duk wata tafiyar aiki, matuƙar sun sanar da hukumar.

Ya ƙara da cewa aikin da aka turo su yi ba wai na diflomasiyya kaɗai ba ne, dama ce ta sanin al’adun Najeriya da kuma ƙarfafa alaƙar tsaro, horaswa, musayar ƙwarewa da sauran fannoni na haɗin gwiwar soja tsakanin Najeriya da ƙasashen su.

Najeriya na ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ‘yan ta’adda, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, da hare-haren wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Sai dai hukumomin tsaro sun ce suna ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *