Amurka ta ce ta fara aiwatar da aniyarta ta hana jiragen da suka taso daga tashoshin jiragen ruwa na Iran wucewa ta Mashigin Hormuz da nufin matsa wa hukumomi a Tehran lamba, bayan da aka tashi tattaunawa a tsakanin bangarorin ta tashi barambaran.
Da karfe 3 na rana agogon Najeriya wa’adin da Shugaba Donald Trump na Amurka ya ayyana ya cika.
A wani sako da ya wallafa a Truth Social, Trump ya yi gargadin cewa, “idan wani daga cikin jiragen kai hari na Iran ya kuskura ya kusanci inda muka kafa shinge, za a batar da shi nan take, ta hanyar amfani irin kisan da muke yi wa masu fataucin kwayoyi a teku”.
Ba Sani, Ba Sabo
Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka ta ce wannan mataki bai shafi kowa bas ai jiragen ruwan da suka taso daga tashoshin jiragen ruwa na Iran.
“Za a aiwatar da wannan shinge ba sani ba sabo a kan jiragen dukkan kasashen da suka shiga ko suka fito daga tashoshin jiragen ruwa na Iran…” inji Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM.
Sai dai Iran ta ce wannan mataki saba yarjejeniyar bude wuta ne kuma zai fuskanci martini mai zafi.
Rundunar Kare Juyin Jiuya-Halin Muslunci ta ce iko da Mashigin Hormuz a hannun Iran yake kuma shingen na Amurka ya haramta.
Matsin Lamba
Masharhanta dai suna ganin Amurka ta dauki wannan mataki ne da nufin matsa wa Iran lamba ta hanyar matsin lamba a kan kasashen da suke sayen manta.
Rahotanni sun ce kusan kashi 30 cikin 100 na danyen man da China take amfani da shi tana saya ne daga Iran – kuma duk da hare-haren da Amurka da Isra’ila suke kaiwa an ci gaba da wannan cinikayya.
Saboda haka fatan Amurka shi ne idan China ta fuskanci matsin lamba za ta mats awa Iran ta koma teburin shawarwari.
Tuni dai darajar hannayen jari ta kasuwannin hadahadar hannayen jari ta Amurka suka fadi, sannan farashin mai ya yi sama.
Shugaban Majalisar Dokoki ta Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya yi gargadi ranar Lahadi cewa matakin zai shafi tattalin arzikin duniya.
“Ku more farashin man fetur yanzu; idan wannan “shingen” ya fara aiki za ku kewar man $4 zuwa $5”.
‘Ba Da Mu Ba’
Kiran da Shugaba Trump ya yi ga wasu kasashe su shiga wannan aiki bai yi nasara ba.
Kasashe kawayen Amurka a Turai sun jaddada cewa ba za su shiga yaki da Iran ba.
Fira Ministan Birtaniya Keir Starmer ya ce tare da hadin gwiwar Shugaba Emmanuel Macron na Faransa zai kira wani babban taron shugabannin duniya don zakulo hanyar bude Mashigin na Hormuz.