Matashin dan wasan Najeriya, Zadok Yohanna, ya shiga cikin jerin sunayen ‘yan takara 100 na kyautar golden boy ta 2026.

A cikin jerin sunayen da aka fitar, matashin yana matsayi na 80 a fafatawar neman kyautar da aka kebe wa ‘yan wasan da ba su wuce shekaru 21 ba a Turai.

Jaridar wasanni ta kasar Italiya mai suna Tuttorsport ce ke gabatar da wannan kyauta kowace shekara tun daga 2003.

Ana bai wa dan wasa mafi fice da bai wuce shekaru 21 kuma yana buga kwallo a daya daga cikin manyan Gasar Turai da UEFA ta amince da su.

Kungiyar manyan ‘yan jaridun kwallo ce ke zabar wanda zai lashe kyautar.

A kwanan nan Zadok ya koma kungiyar Brighton & Hove Albion na Ingila daga AIK stockholm na Sweden, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar wanda zai kare a watan yuni na 2031.

Zadok ya fara buga kwallo a kungiyar Ikon Allah football academy a Najeriya, kafin ya koma Sweden a 2025 ya shiga AIK, inda ya yi saurin koyan salon taka leda na kasar Turai.

A wannan kaka, ya buga wasanni 18 da AIK, inda ya zura kwallaye 5 ya kuma bayar da taimakon cin kwallo 4.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *