Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato ta ce ta ƙwato dabbobi 689 da ‘yan bindiga suka sace a sassa daban-daban na jihar, sakamakon hare-haren da jami’anta suka dakile tsakanin watan Mayu zuwa yanzu.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Hayatu Hassan Shaffa ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a Sakkwato, inda ya ce an gudanar da samamen ne a ƙananan hukumomin Tangaza da Wamakko da Tureta da Bodinga.
- Kotu: Malami ya kasa tabbatar da asalin kuɗin sayen kadarori 48
- Tinubu ya ƙaddamar da rukunin samar da ruwa na Bwari, Ya yi kardadon faɗaɗa samar da ruwa a FCT
Ya ce jami’an rundunar sun yi artabu da ‘yan bindigar a lokuta daban-daban, inda suka ƙwato dabbobin tare da kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi.
Shaffa ya ƙara da cewa an mayar da dabbobin da aka ƙwato ga masu su, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.