A halin yanzu, rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sakkwato ta ce ta kama mutane da dama da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci, ciki har da masu garkuwa da mutane da masu bai wa ‘yan bindiga bayanan sirri da masu kai musu man fetur da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Hayatu Hassan Shaffa, ya ce daga cikin waɗanda aka kama akwai mutane uku da suka amsa laifin shiga ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar wasu ƙananan hukumomi a jihar.
- ‘Yan sanda sun ƙwato dabbobi 689 daga hannun ‘yan bindiga a Sakkwato
- ‘Yan sanda sun ƙwato dabbobi 689 daga hannun ‘yan bindiga a Sakkwato
Ya ce jami’an rundunar sun kuma kama wani da ake zargi da kai wa ƙungiyar Lakurawa man fetur da sauran kayayyaki, inda aka ƙwato galan-galan na fetur da tabar wiwi da ƙwayoyin Tramadol.
Shaffa ya ƙara da cewa rundunar ta kuma kama wasu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma masu satar babur.
Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin yaƙi da miyagun laifuffuka a fadin jihar.