Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan Dokar Zartarwa ta Shugaban Ƙasa kan Daidaita Harkokin Kuɗaɗen Dijital ta shekarar 2026, domin inganta tsarin sa ido da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati masu kula da wannan fanni.
Sanarwar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce dokar ta fara aiki nan take.
- ‘Yan sanda sun kama masu garkuwa da masu bai wa ‘yan bindiga bayanai da masu safarar miyagun ƙwayoyi
- Ɓunƙasa Ilimi da rage talauci: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirye-shirye biyar na bankin Duniya
Ta ce matakin zai taimaka wajen kare ‘yan ƙasa daga damfara, da hana safarar kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya da dakile tallafa wa ta’addanci da kuma kare tsarin kuɗin ƙasar, tare da bai wa sabbin fasahohin dijital damar bunƙasa cikin tsari.
Sanarwar ta ƙara da cewa dokar ba ta kafa sabuwar hukuma ba, illa dai ta samar da tsarin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da suka riga suke da ikon doka a wannan fanni.