Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, na samun sauye-sauye masu kyau ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike a matsayin Minista, shekaru 50 bayan kafa babban birnin.
Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja a daren Juma’a yayin wani liyafar godiya ta musamman domin murnar kammalawa da ƙaddamar da ayyuka 31 a cikin kwanaki 28 a faɗin babban birnin
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wanda ya wakilci shugaban ƙasa, ya yaba wa Wike da tawagarsa saboda ƙoƙarin da suka yi wajen tabbatar da cewa babban birnin ƙasar yana aiki yadda ya kamata domin amfanin dukkan ‘yan Najeriya.
- wamnatin Najeriya ta kafa majalisar kula da harkokin kuɗaɗen dijital, CBN za ta jagoranta
- Tinubu ya rattaba hannu kan dokar da za ta daidaita harkokin kuɗaɗen dijital
- Tinubu ya umarci a samar da tsarin aiwatar da dokar kuɗaɗen dijital cikin kwanaki 30
Ya kuma yaba wa ministan, yana mai cewa ya nuna cewa: “Ba yawan sanar da tsare-tsare ke nuna nagartar shugabanci ba, sai dai irin sakamakon da jama’a ke gani a aikace.”
Tinubu ya ce Abuja mallakin kowa ne ɗan Najeriya ne, yana mai bayyana ta a matsayin birnin da ke haɗa kan ƙasa, inda bambance-bambance ke haɗuwa, kuma inda buri da fata na kowane ɗan ƙasa ke samun matsuguni.