Kyaftin din Argentina Lionel Messi, ya yi tsokaci a bainar jama’a kan hoton da aka ganshi yana yiwa wani jariri Yamal Lamine wanka a filin wasa na Camp Nou, Barcelona.
Yanzu kusan shekaru 20 kenan baya, inda Messi ya bayyana lamarin da “abin mamaki.”
Yayin wani taro da Tom Brady a birnin New York na Amurka, Kyaftin ɗin na Argentina ya ce “wannan ita ce rayuwa, ko ba haka ba? Na ɗauki hoto da shi yana karami, yanzu ga shi mu biyun za mu fuskanci juna a wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya.”
-
Karambatta tsakanin Joshua da Itauma a Najeriya zai dauki hankalin duniya—Ezekiel Adamu
-
Atlético Madrid ta ce Julián Álvarez ba na sayarwa ba ne
-
Flying Eagles za ta fara kare kambun WAFU B akan Ghana
A ranar Lahadi Argentina za ta kara da Spaniya a wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya na 2026 a filin was na MetLife Stadiya.
“Lamine babban haziƙin dan wasa ne. Ina bibiyan wasansa sosai saboda yana wasa a ƙungiyar da nake so. Ina yi masa fatan alheri kullum. Yanzu yana da shekaru 19 kuma yana ɗaya daga cikin mafi kyawun ɗan wasa a duniya,” in ji Messi.
“Yana da babbar dama na kafa tarihi, amma za mu yi kokarinmu saboda kadda hakan ya faru a wannan karon. Ina masa fatan alheri kawai.”
A nasa ɓangaren, Yamal ya yi dariya a lokacin da aka tambaye shi kan hoton, inda ya ce “Gaskiya na yi mamaki saboda Messi yana riƙe da ni a hannunsa, ni kuma ban kalleshi ba. Ban san me nake yi ba, amma ina farin ciki sosai da na ɗauki hoto da mafi kyawun dan wasa a tarihi.”
Yamal ya ƙara da cewa dukaninsu su biyun sun ƙara manyanta tun bayan ɗaukar hoton, sa’annan kuma ya musanta ra’ayin al’umma da ke cewa dole ne ya zamanto kamar Messi.
“Dukkannin mu mun san ba na son na zama Messi, kuma Messi ya san ba na son zama kamar shi. Ina son bin irin tawa hanyar, shine kawai,” a cewar Yamal.
