Dakarun Operation HAƊIN KAI (OPHK) tare da haɗin gwiwar jami’an Rundunar ‘Yan Sandan sun daƙile wani yunƙurin da ‘yan ta’addar ISWAP suka yi na sace ɗalibai a Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya ta ‘Yan Mata (FGGC) da ke Monguno.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar 19 ga Yuli, 2026.

A cewar wata sanarwa da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labaran Soji, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ‘yan ta’addar sun samu shiga harabar makarantar ne da taimakon wasu da ake zargi da nufin yin garkuwa da ɗaliban.

Sai dai jami’an tsaro da ke bakin aiki sun gaggauta mayar da martani tare da buɗe musu wuta, yayin da Rundunar ta 3 (Quick Reaction Force – QRF) ta isa wurin domin ƙarfafa dakarun da ke fafatawa.

Bayan kammala farmakin, dakarun sun ceto tare da kwashe ɗalibai 46 zuwa Barikin Kinnasara da ke Monguno, inda aka yi musu gwajin lafiya tare da ba su kulawar da ta dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *