Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ɗora bayanan ɗan takararta na wucin gadi na shugaban ƙasa na zaɓen 2027 da kuma sunayen ’yan takarar Majalisar Dokoki ta Ƙasa guda 355 a shafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) duk da ƙarancin lokacin da aka ba ta
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Agbo Major, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja
- Obi ya amince zai yi wa’adi ɗaya idan aka zaɓe shi — Kwankwaso
- Gwamnatin Tarayya ta farfaɗo da dakunan karatu na intanet (e-libraries) 16 da aka watsar a Kano
- Ma’aikatar Tsaro ta musanta jita-jitar murabus ɗin Minista Christopher Musa
Major ya bayyana wannan nasara a matsayin tarihi, duba da ƙuntataccen lokacin da jam’iyyar ta samu bayan jinkirin da INEC ta yi wajen bin umarnin kotu na amincewa da sahihin shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin wanda ya kafa ta, Dr. Boniface Aniebonam.
Ya kuma tabbatar da cewa INEC ta mayar da asalin suna da tambarin NNPP, wanda ya ƙunshi kwandon ’ya’yan itatuwa a kan taswirar Najeriya, a cikin shafin gabatar da sunayen ’yan takarar
Ya ƙara da cewa an fara ɗora sunayen ’yan takarar gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi, kuma ana sa ran za a kammala hakan kafin 8 ga Agusta lokacin da wa’adin sauya sunayen ’yan takara zai ƙare
Sai dai Major ya soki INEC bisa abin da ya kira rashin bin umarnin kotu akan lokaci, yana mai cewa jinkirin ya haifar wa jam’iyyar matsaloli wajen shirye-shiryenta na zaɓen 2027.