A ranar Jumma’a, Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya karɓi baƙuncin tawagar ‘yan wasan mata ta Jihar, Nasarawa Amazons, waɗanda suka lashe kofin FA ta Mata na 2026, a fadarsa dake Lafia.
Idan za a iya tunawa Nasarawa Amazons sun doke Heartland Queens 6-5 a bugun fenareti a wasan ƙarshe a gasar FA ta Mata bayan sun tashi a cikin fili 1-1 a garin Asaba, ranar 11 ga watan Yuli, 2026.
Da yake yabawa ‘yan wasan matan Amazons, Gwamna Sule ya sanar da ba su kyautar mota ƙirar bas mai kujeru 38, sa’an nan da kyautar kuɗi naira miliyan 25 ga ‘yan wasa 36 da aka yiwa rajista.
-
Gwamnatin Tarayya ta baiwa tawagar ‘yan wasan ɗaga nauyi na masu buƙata ta musamman kyautar kuɗaɗe
-
Super Falcons za ta fara kare kambunta na WAFCON akan Malawi ranar Lahadi
-
Jamus ta naɗa Jurgen Klopp a matsayin sabon kocin Tawagar Kasar
Har ila yau, Gwamna Sule ya bai wa ‘yan wasanni biyu da suka fi bajinta, Hembafan Ayatsea da Udoka Unchukwu kyautar kuɗi dala dubu ɗaya kowacce, yayin da ya bai wa sauran ‘yan wasannin kyautar dala ɗari biyar.
Gwamnan ya kuma bai wa masu horar da ‘yan wasan kyautar kuɗi naira miliyan 15, kana kuma ya bai wa ƙungiyar magoya baya kyautar naira miliyan 5.
Gwamna Sule ya kuma bai wa ƙungiyar Maza ta Nasarawa United, waɗanda suka ƙare a matsayi na 6 a gasar NPFL ta bara 2025/26 kuma suka kai matakin wasan kusa da na ƙarshe na kofin FA kyautar kuɗi naira miliyan 10. Sa’an nan suma ɓangaren ‘yan wasan da ake yayewa zuwa babban tawagar na maza sun samu kyautar naira miliyan 10.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta jihar ita ma ta samu kyautar naira miliyan 10, yayinda shi ma Jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar wasanni ta jihar, Mr Eche Amos, ya samu kyautar dala ɗari biyar.