Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ayyana shekarun 2027 zuwa 2036 a matsayin shekaru goma na ƙarfafa zaman lafiya ga al’ummomin da za su zo nan gaba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa wannan mataki ya biyo bayan amincewar Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya da wani ƙuduri da ya samar da tsari na shekaru 10, domin bunƙasa zaman lafiya, haɗin gwiwa da ci gaba mai ɗorewa.

Shugaban Tajikistan, Emomali Rahmon, ne ya gabatar da wannan yunƙuri, wanda manufarsa ita ce ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe, ƙara bai wa matasa damar shiga harkokin yanke shawara da kuma bunƙasa haɗin kan al’umma.

Hakan ya sake jaddada ƙudurin ƙasashe ga bin ƙa’idojin Yarjejeniyar MDD, da kuma sanarwa da shirin samar da al’adar zaman lafiya, tare da ƙarfafa shirye-shiryen da za su gina amincewa da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe.

Ya kuma mai da hankali kan shigar da yara da matasa cikin harkokin jama’a da ƙarfafa matakan gina amincewa da juna, da kuma tallafa wa ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Jakadan Tajikistan a Rasha, Davlatshoh Gulmahmadzoda, ya bayyana cewa wannan yunƙuri an tsara shi ne domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe da kuma magance matsalolin da ke shafar al’ummomin gaba.

Ya ce wannan shekaru goma za su taimaka wajen cika manufofin taron ‘Summit of the Future’ na 2024 da kuma ‘Pact for the Future’ da aka amince da su yayin taron.

Wannan yunƙuri ya kuma yi daidai da manufofin jin ƙai na ƙungiyar BRICS, musamman wajen inganta haɗin gwiwar ƙasashe da ci gaba mai ɗorewa da musayar ayyukan jin ƙai.

Dukkan ƙasashe mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya, ciki har da ƙasashen BRICS da abokan hulɗarsu, sun amince da ƙudurin, abin da ke nuna goyon bayan duniya wajen ciyar da zaman lafiya da haɗin gwiwa gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *