Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da rufe makarantun boko a kananan hukumomi 20 daga cikin 23 da jihar ke da su.
Sanarwar da aka aiwakawa shugabannin makarantu wadda Sakataren hukumar kula da makarantu ya sanya wa hannu, ya ce makarantun da ke ƙananan hukumomin Sakkwato ta Kudu da Sakkwato ta Arewa da wasu makarantu da aka zaɓa a ƙananan hukumomin Wamakko da Dange Shuni za su ci gaba da karatu ba sa cikin waɗanda aka rufe.
- Fubara bai yi wani laifi ba — Wike
- Kotun ɗaukakaƙara ta soke hukuncin da ya umarci a soke rajistar ADC, Accord da sauran Jam’iyyu
- Na gamsu da yadda aka zamanantar da NTA — Minista
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa wani malami da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an sanar da su an rufe makaranta ciki har da wadda yake karantarwa.
Ya ce suna ganin an rufe makarantun ne saboda matsalar tsaro da ke ƙara yawaita a jihar, ganin kullum sai ’yan bindigar sun shiga gari ko ƙauye a yankin Gabas ko kudancin jihar Sakkwato.
Jihar Sokoto dai ta dade tana fama da matsalar ɓarayin daji da suke sace mutane domin karɓar kuɗin fansa. Ko a watan maris na 2024 ;yanbindigan sun sace ɗaliban makarantar Islamiyya 17 ƙauyen Gidan Bakuso, da ke Ƙaramar Hukumar Gada.