Majalisar Dokokin Aljeriya ta zaɓi Khalida Boufedeche a matsayin mace ta farko da ta zama Shugabar Majalisa a zaɓen da aka gudanar a ranar Talata.

Nadin Khalida Boufedeche, wacce ƙwararriyar likita ce, kuma takę wakiltar babban birnin ƙasar, Algiers, a Majalisar Dokoki., ya sanya ta zama a mataki na huɗu mafi girman matsayi a tsarin mulkin ƙasar.

Shugabar ta kasance mamba a tsohuwar jam’iyyar da ta jagoranci gwagwarmayar neman ‘yancin kai a Aljeriya, wadda har yanzu tana da karfin fada-a-ji a fagen siyasar ƙasar.

Jam’iyyarta ta zama mafi rinjaye a zaɓen Majalisar Dokoki da aka gudanar a farkon watan Yulin shekarar 2026, bayan da ta lashe kujeru 91 daga cikin kujeru 407 na majalisar.

Sai dai zaɓen ya kasance mafi ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a tarihin Aljeriya, inda kashi 21 cikin 100 ne kadai na masu rajistar zaɓe suka fito domin kada kuri’a.

Kafin shiga majalisar dokoki, Boufedeche ta riƙe muƙamai daban-daban na siyasa a matakan ƙaramar hukuma, sannan tana daga cikin mambobin kwamitin zartaswa na uwar jam’iyyar ta.

Shugabar, ta karɓi shugabancin majalisar ne a lokacin da yawan mata ke ci gaba da raguwa a zauren majalisar dokokin ƙasar. A halin yanzu, mata na da kujeru 25 kacal daga cikin kujeru 407, wanda ya kai kusan kashi shida cikin ɗari na adadin kujerun majalisar.

Wannan adadi ya yi ƙasa idan aka kwatanta da majalisar da ta gabata wadda ke da mata mambobi 38. Haka kuma, bayan zaɓen shekarar 2017, majalisar ta taɓa samun mata 118 sakamakon tsarin ware wasu kujeru na musamman domin ƙarfafa wakilcin mata a siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *