Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) a halin yanzu tana gudanar da aikin tantance sakamakon jarrabawar rubutu ga masu neman aiki a Rundunar ‘Yan Sanda ta Nijeriya. Ana gudanar da wannan aiki ne a babban sakatariyar hukumar da ke Abuja.
Wata sanarwa da aka fitar a shafin facebook na rundunar ta ce annan tsari na tantancewa da aka gina shi a kan cancanta, an tsara shi ne domin tabbatar da cewa gwanaye kuma cancantattun ‘yan takara ne kawai za su tsallaka zuwa mataki na gaba na aikin daukar ma’aikatan.
- Gwamna Oyebanji ya yi Ƙarin alƙawura ga mazauna jihar Ekiti.
- Wane ne Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Ekiti?
- Ƙungiyar Matasa Ta Yi Alƙawarin Mara Wa Sojoji Baya, Ta Nemi Ƙarin Haɗin Kai
Wakilan Rundunar ‘Yan Sanda ta Nijeriya, Ma’aikatar Al’amuran ‘Yan Sanda, da Hukumar Halayyar Tarayya (Federal Character Commission) suna sanya ido sosai kan yadda tsarin ke tafiya domin tabbatar da adalci, gaskiya, da kuma gamsarwa.
Ana kyautata zaton za a kammala aikin tantancewar nan da ‘yan kwanaki masu zuwa. Daga nan ne kuma za a gayyaci ‘yan takarar da suka yi nasara domin tantance lafiyarsu (medical screening), kafin daga bisani a fitar da sunayen wadanda suka yi nasara na karshe gabanin fara horon ‘yan sanda (constable training).
Ana shawartar masu neman aikin da su kwantar da hankalinsu kuma su saurari bayani na hukuma daga hukumomin da abin ya shafa.