Gwamnatocin kasashen Isra’ila da Lebanon sun amince su tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki 10, domin baiwa tattaunawar diflomasiyya dama.
Sanarwar ta fito ne daga fadar White House a yau Alhamis, inda shugaba Trump ya wallafa a shafin sa na Truth Social, yana umartar shugabannin kasashen biyu su bayyana a fadar.
Shugaban Amurka Donald Trump wanda shi ne ya jagoranci sulhun, ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta fara aiki ne da misalin karfe 5:00 na yamma agogon Amurka, wanda ya yi daidai da karfe 10 na dare a najeriya.
Bayanai dake fitowa daga gabas ta tsakiya na na cewa bangarorin biyu sun amince su daina harba makamai masu linzami da kai hare-hare akan juna. Inda Amurka zata yi amfani da tsawon kwanaki 10 domin tabbatar da babu bangaren da ya keta yarjejeniyar.
Shugaba Trump ya bayyana cewa ya tattauna kai-tsaye da Firayminista Benjamin Netanyahu da kuma shugaban Lebanon Joseph Aoun, dukkaninsu sun aminta da bukatar hakan.
Duk da wannan murna, masana na sanya shakku kan ko kungiyar Hezbollah za ta amince da wannan tsari, duba da cewa har yanzu akwai takaddama kan wasu yankuna a kan iyaka. Sai dai gwamnatin Lebanon ta ba da tabbacin cewa za ta yi iyakacin kokarinta wajen ganin an kiyaye dokar.
