Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta zargi dakarun Africa Corps na Rasha da ke taimaka wa gwamnatin Mali wajen yaki da masu tayar da kayar baya da kashe fararen hula takwas, ciki har da kananan yara uku, a hare-haren sama da aka kai a watan Yuni.
A cikin wani rahoto da kungiyar ta fitar ranar Juma’a, ta ce jirgin yaki kirar Sukhoi Su-24 ya jefa akalla bama-bamai biyu a kauyen Kyrnia da ke yankin Mopti a ranar 15 ga Yuni.
Rahoton ya ce bam na farko ya fado a wajen gidan shugaban kauyen, inda ya kashe ‘ya’yansa biyu, da matarsa da wani yaro, tare da jikkata wata mata.
- Liberia ta ƙona hodar iblis mai nauyin tan 4.2
- A karon farko an zabi mace ta shugabanci Majalisar Dokokin Aljeriya
- Guinea da Gabon sun warware tsohuwar takaddamar dake tsakanin su
Bam na biyu kuma ya fado a wata karamar kasuwar shanu da ke kusa da wurin, inda ya kashe maza hudu tare da jikkata wasu biyu.
HRW ta ce babu wani mayaƙin kungiyar masu ikirarin jihadi da ya rasa ransa a harin.
A cikin ‘yan watannin nan, mayaƙan ƙungiyar masu neman ballewar Tuareg ta FLA da kuma ƙungiyar JNIM, mai alaƙa da Al-Qaeda, sun kai hare-hare da dama kan gwamnatin mulkin soji ta Mali da kuma dakarun Rasha da ke mara mata baya
Babbar mai bincike kan yankin Sahel ta HRW, Ilaria Allegrozzi, ta ce gwamnatin Mali ba za ta iya kauce wa alhakin abin da ƙawayenta ke aikatawa ba.
Sai dai kungiyar Africa Corps ta ɗauki alhakin harin a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta ce wurin da aka kai harin mafakar ‘yan ta’adda ne.
Sai dai shaidu da HRW ta tattauna da su sun bayyana cewa sama da mayaƙan JNIM 100, ciki har da wani babban kwamanda, suna cikin kauyen lokacin da aka kai harin.
Tun daga 2012 Mali ke fama da matsalar tsaro, kuma shugabannin mulkin sojan ƙasar sun yi alƙawarin dawo da zaman lafiya bayan karɓe mulki ta juyin mulki a shekarun 2020 da 2021.
Bayan hawansu mulki, gwamnatin sojin ta rage alaƙarta da ƙasar da ta yi mata mulkin mallaka, Faransa, tare da ƙara kusanci da Rasha a fannin tsaro da siyasa.