Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakiya da Ƙasa (NMDPRA) ta ce lokaci ya yi da Afirka za ta samar da nata tsarin ma’aunin farashin man fetur, domin rage dogaro da farashin da ake amfani da su daga ƙasashen waje tare da ƙarfafa kasuwar makamashi a nahiyar.
Shugaban NMDPRA kuma shugaban ƙungiyar hukumomin kula da harkokin man fetur na Yammacin Afirka (WARF), Mallam Rabiu Abdullahi Umar, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a gabanin taron kasuwar tataccen man fetur na nahiyar Afrika mai zuwa.
Ya ce yadda ake ƙara samun matatun mai a Afirka ya nuna muhimmancin samar da tsarin farashi na cikin gida wanda zai dace da yanayin kasuwar nahiyar, ya ƙara bayyana gaskiya a harkar ciniki da kuma taimaka wa wajen jawo ƙarin zuba jari.
- ‘Yan sanda sun dakile harin ‘yan bindiga jihar sokoto
- ABU da NAHCON sun sanya hannu kan fara digiri a fannin gudanar da aikin Hajji
- ‘Yan sanda sun ceto yaro ɗan shekara 9 da aka sace a Kano
A cewarsa, dogaro da ma’aunin farashi na ƙasashen waje na iya rage damar da Afirka ke da ita wajen cin gajiyar albarkatun makamashinta, musamman yayin da ƙasashen nahiyar ke ƙara ƙarfin tace man fetur.
Mallam Rabiu ya bayyana cewa taron, wanda za a gudanar daga ranar 11 zuwa 12 ga Agusta tare da haɗin gwiwar S&P Global Commodity Insights da WARF, zai zama wata dama ta tattauna hanyoyin cike gibin da ke akwai a harkokin more rayuwa da jawo masu zuba jari da kuma samar da ingantaccen tsarin farashin man fetur na Afirka.
NMDPRA ta ce samar da irin wannan tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen Yammacin Afirka da kuma bai wa nahiyar damar samun cikakkiyar fa’ida daga haɓakar masana’antar tace man fetur.