Jam’iyyar ADC ta ce wa’adin mulkin dukkan sababbin shugabannin da aka zaba ba zai fara aiki ba har sai an rantsar da su a ranar 12 ga watan Mayun shekarar 2026.

A wata sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Kasa Mallam Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta jaddada cewa tsofaffin shugabanni ne kadai aka sani a halin yanzu har sai lokacin da wa’adin su ya cika.

Jam’iyyar ta sanya ranar 12 ga watan Mayun wannan shekarar a matsayin ranar rantsar da sababbin shugabannin matakin jihohi da sauran  ofisoshi.

A saboda haka ta ja kunnen sababbin shugabannin da su guji bayyana kansu a matsayin masu iko ko yin katsalandan a harkokin jam’iyya har sai an ba su iko a hukumance.

Jam’iyyar ta ce tana yin hakan ne domin tabbatar da bin tsarin mulki, oda, da kuma kaucewa duk wani rudani da zai iya tasowa a tsarin gudanarwarta.

Malam Bolaji ya jaddada cewa ADC jam’iyya ce mai bin doka da oda, kuma tana sa ran dukkan mambobinta za su bi wannan umurni domin dorewar zaman lafiya da ci gaban jam’iyyar.

A farkon ranar Talatar da ta gabata ne ADC ta yi babban taron ta na kasa anan Abuja, inda ta zabi sabbin shugabanni karkashin tsohon shugaban ta na riko Sanata David Mark, har ta sha alwashin kawo karshen mulkin APC a babban zabe mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *