Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta wallafa sunaye da bayanan sirri na ‘yan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu da za su fafata a zaɓen shekarar 2027.
Daga cikin fitattun ‘yan takarar da aka bayyana akwai Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar na ADC, da kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi na NDC.
Sai dai sunan tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan, wanda ɓangaren Tanimu Turaki na PDP ya tsayar takara, bai bayyana a jerin sunayen da INEC ta fitar ba. A maimakon haka, an wallafa sunan Sanata Sandy Onor, wanda ɓangaren PDP mai goyon bayan Nyesom Wike ya tsayar.
- Sojoji sun daƙile harin ‘yan ta’adda a Kasuwar Daji, sun ceto mutane 9
- Rukunin farko na dakarun wanzar da zaman lafiya sun isa Guinea-Bissau – NAF
- Jigawa – Gwamnati ta ware naira biliyan 13 domin magance zaizayar Ƙasa
Haka kuma, sunan Gbenga Olawopo Hashim, wanda ya yi iƙirarin cewa shi ne ɗan takarar jam’iyyar Accord, bai shiga jerin sunayen ba.
Tun da farko jam’iyyar Accord ta bayyana cewa ba ta da ɗan takarar shugaban ƙasa saboda babu wanda ya cika wa’adin gabatar da takara.
Jam’iyyun siyasa ne dai suka gabatar da sunaye da bayanan ‘yan takararsu da suka yi nasara a zaɓen fidda gwani ga INEC.
Takardun da aka gabatar sun haɗa da fom din EC9 A-E, shaidun karatu, takardar kammala aikin NYSC da takardar rantsuwa daga Babbar Kotun Tarayya da tarihin aiki da sauran muhimman bayanai.
Takardun Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun nuna cewa yana da digirin farko a fannin Gudanar da Harkokin Kasuwanci (Business Administration) daga Jami’ar Chicago da ke Amurka.
Haka kuma, Peter Obi da Donald Duke da Omoyele Sowore sun bayyana cewa suna da irin wannan digiri.
A cikin bayanansa, Tinubu ya ce an haife shi ne ranar 29 ga Maris, 1952, a Lagos. Ya yi aiki da kamfanin Mobil Nigeria Limited tsakanin shekarun 1983 zuwa 1992 kafin ya shiga siyasa, inda ya zama Gwamnan Jihar Lagos daga 1999 zuwa 2007.
Ya kuma bayyana cewa aikinsa na yanzu shi ne na Gwamnatin Tarayyar Najeriya, tare da tabbatar da cewa ba a taba korarsa daga aikin gwamnati ba.