Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa za a sake zaman tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a yammacin ranar Litinin, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa za a iya cimma yarjejeniya kan mashigin ruwan Strait of Hormuz da kuma batun dakatar da shirin nukiliyar Iran

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a cikin jirgin shugaban kasa Air Force One, yayin da yake kan hanyar zuwa Joint Base Andrews da ke jihar Maryland

Ya ce tattaunawar da aka yi da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar da kuma Iran ce ta sa ya soke wani gagarumin hari da aka shirya gudanarwa a ranar Juma’a data gabata

“Ba su so mu kai harin ba, kuma a gaskiya Saudiyya ma ba ta so hakan. Sun yi imanin cewa yarjejeniya ta kusa kammaluwa, musamman kan mashigin Hormuz da kuma batun kawar da shirin nukiliyar Iran,” in ji Trump.

Trump ya kara da cewa kasashen uku da kuma Iran sun bukaci Amurka da ta ci gaba da tattaunawa maimakon daukar matakin soji

Idan dai za a iya tunawa a ƙarshen makon daya gabata ne wani janar nasojin Amurka dake jagorantar rundunar dake yaƙi  da iran ya bayyana cewa basu da isassun ƙarfin da zasu iya baiwa Isra’ila kariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *