Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

An haifi Asiwaju Bola Ahmed Adekunle Tinubu a ranar 29 ga Maris, 1952, a birnin Legas. Mahaifiyarsa ita ce Abibatu Mogaji, wadda ta taba zama Ìyál’ọ́jà (shugabar kasuwannin Legas).

Tinubu ya yi karatun farko a kudu maso yammacin Najeriya kafin ya tafi Amurka, inda ya karanci Lissafin Kuɗi (Accounting) a Jami’ar Chicago State University,

Bayan dawowarsa Najeriya a shekarun 1980, ya yi aiki a kamfanin Mobil Nigeria a matsayin akanta.

Ya shiga siyasa a shekarar 1992, inda aka zaɓe shi, sanatan Legas ta Yamma, a ƙarƙashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP).

Bayan soke zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1993 da kuma karɓe mulki da Janar Sani Abacha ya yi, Tinubu ya shiga ƙungiyar fafutukar dawo da dimokuraɗiyya ta National Democratic Coalition (NADECO)

An taba tsare shi na ɗan lokaci saboda ayyukansa na fafutukar dawowar mulkin dimokuraɗiyya, kafin daga bisani ya tsere zuwa gudun hijira a shekarar 1994. Ya komo Najeriya ne bayan rasuwar Janar Abacha a shekarar 1998.

A shekarar 1999, Tinubu ya tsaya takarar gwamnan Jihar Legas a ƙarƙashin jam’iyyar Alliance for Democracy (AD), inda ya yi nasara. An sake zaɓensa karo na biyu a shekarar 2003 zuwa 2007.

Bayan kammala wa’adinsa a shekarar 2007, tasirin Tinubu a siyasar Najeriya ya ƙaru sosai, inda aka fara masa laƙabi da “uban siyasa” (Political Godfather) saboda rawar da yake takawa wajen mara wa ‘yan takara baya da kuma taimakawa wajen zaɓen shugabanni a matakai daban-daban.

A shekarar 2013, ya kasance cikin jagororin da suka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Ya kuma mara wa Muhammadu Buhari baya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2015, wanda Buhari ya lashe, sannan ya sake samun nasara a zaɓen 2019.

A 2023, an zabi Bola Ahmad Tinubu a matsayin Shugaban Najeriya, karkashin tutar jam’iyyar APC. Wa’adinsa na farko na gab da karewa, inda a yanzu haka, yake kokarin sake shiga zaben 2027. Tuni APC ta tabbatar masa da takarar, inda shi kuma ya sake daukar mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda za su rankaya tare don sake neman kuri’un ‘yan Najeriya a babban zaben 2027.

 

 

Atiku Abubakar

An haifi Atiku Abubakar a ranar 25 ga Nuwamba, 1946 a garin Jada, wanda a lokacin yana cikin yankin British Cameroons kafin daga baya ya kasance cikin Najeriya, bayan zaɓen haɗewar yankin British Cameroons da Najeriya a shekarar 1961.

Mahaifinsa, Garba Abubakar, ɗan kasuwa ne, Bafulatani kuma manomi,; yayin da mahaifiyarsa ita ce Aisha Kande. An sanya masa suna ne da sunan kakansa na wajen uba, Atiku Abdulqadir, wanda ya fito daga Wurno a Jihar Sokoto sannan ya yi hijira zuwa ƙauyen Kojoli da ke Jada, Adamawa.

Lokacin da yake da shekara takwas, Atiku ya fara karatu a Makarantar Firamare ta Jada, Adamawa. Bayan ya kammala firamare a shekarar 1960, ya shiga Makarantar Sakandaren Lardin Adamawa tare da wasu ɗalibai 59. Ya kammala sakandare a shekarar 1965, bayan ya samu sakamako na Grade Three a jarrabawar kammala sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC).

Bayan kammala sakandare, Atiku ya ɗan yi karatu a Kwalejin ’Yan Sanda ta Najeriya da ke Kaduna. Sai dai ya bar makarantar saboda rashin samun takardar sakamakon lissafi a matakinn O’ Level. Daga nan ya yi aiki na ɗan lokaci a matsayin jami’in haraji a Ma’aikatar Kuɗi ta yankin.

A shekarar 1966 ya samu gurbin karatu a Makarantar Kiwon Lafiya ta Kano, inda ya kammala Diploma a shekarar 1967. A lokacin karatunsa ya taɓa zama shugaban ƙungiyar ɗalibai na wucin gadi.

A shekarar 1967, ya shiga Cibiyar Gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi karatun Diploma a fannin Shari’a bisa tallafin gwamnatin yankin. Bayan kammala karatunsa a shekarar 1969, lokacin yaƙin basasar Najeriya, ya fara aiki da Hukumar Kwastam ta Najeriya.

A shekarar 2021, Atiku Abubakar ya kammala digirinsa na biyu (Master’s Degree) a fannin Hulɗar Ƙasa da Ƙasa daga Jami’ar Anglia Ruskin da ke Birtaniya.

Atiku ya yi aiki a Hukumar Kwastam ta Najeriya na tsawon shekaru 20, inda ya kai matsayin Mataimakin Darakta, wanda a lokacin shi ne matsayi na biyu mafi girma a hukumar. Ya yi ritaya daga aikin a watan Afrilu na shekarar 1989, sannan ya shiga harkokin kasuwanci da siyasa gaba ɗaya.

Ya fara shiga siyasa ne a shekarar 1980 inda ya taimaka a bayan fage wajen yaƙin neman zaɓen gwamnan Bamanga Tukur, wanda a lokacin shi ne shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA).

To sai dai kafin nan a ƙarshe-ƙarshen aikinsa na Kwastam, Atiku ya haɗu da Janar Shehu Musa Yar’Adua, wanda ya riƙa jawo shi cikin tarukan siyasa da ake gudanarwa a gidansa da ke Legas, waɗanda daga baya suka haifar da ƙungiyar siyasa ta People’s Front of Nigeria

A shekarar 1989, an zaɓi Atiku a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa na ƙungiyar People’s Front of Nigeria. Haka kuma ya samu kujerar wakilcin mazabarsa a Majalisar Tsarin Mulki ta shekarar 1989 da aka kafa domin tsara sabon kundin tsarin mulkin Najeriya

Daga baya gwamnatin soji ta hana rajistar ƙungiyar, sannan aka haɗa ta da jam’iyyar Social Democratic Party (SDP)

A ranar 1 ga Satumba, 1990, Atiku ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan tsohuwar Jihar Gongola. Amma kafin zaɓe, gwamnatin tarayya ta raba Gongola zuwa Jihohin Adamawa da Taraba, inda Atiku ya samu kansa a Adamawa.

A watan Nuwamban shekarar 1991 ya lashe zaɓen fidda gwani na SDP, amma gwamnati ta hana shi tsayawa takara.

A shekarar 1993, Atiku ya nemi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar SDP, sai dai a zagayen farko na zaɓen fidda gwani da aka gudanar a Jos, Moshood Abiola ya samu ƙuri’u 3,617, Baba Gana Kingibe ya samu 3,255, yayin da Atiku ya samu 2,066.

Atiku da Kingibe sun yi tunanin haɗa ƙarfi domin kalubalantar Abiola, amma bayan shawarar Shehu Yar’Adua, Atiku ya janye takararsa, inda aka yi masa alƙawarin cewa Abiola zai zaɓe shi a matsayin abokin takara. Sai dai daga baya aka matsa wa Abiola ya zaɓi Baba Gana Kingibe a matsayin mataimakinsa a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993

Bayan zaɓen 12 ga Yuni da kuma lokacin gwamnatin Janar Sani Abacha, Atiku ya nuna sha’awar neman kujerar gwamnan Adamawa karkashin jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP). Sai dai shirin mika mulki ya tsaya bayan rasuwar Janar Abacha.

A shekarar 1998, Atiku ya shiga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), inda daga baya ya samu tikitin takarar gwamnan Adamawa. Ya lashe zaɓen gwamna a watan Disamba na shekarar 1998.Amma kafin a rantsar da shi a matsayin gwamna, ya amince ya zama abokin takarar shugaban ƙasa na PDP, tsohon shugaban mulkin soja Janar Olusegun Obasanjo. Su biyun sun lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1999.

A zaɓen shugaban ƙasa na 2007, ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Action Congress (AC), inda ya zo na uku bayan Umaru Musa Yar’Adua na PDP da Muhammadu Buhari na ANPP.

A shekarar 2011, ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), amma ya sha kaye a hannun shugaban ƙasa mai ci a wancan lokacin, Goodluck Jonathan.

Gabanin zaɓen shekarar 2015, Atiku ya fice daga PDP ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC), inda ya nemi tikitin takarar shugaban ƙasa, amma ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari.

A shekarar 2017, ya koma jam’iyyar PDP, sannan ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2019, inda ya sake shan kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari.

A watan Mayun 2022, jam’iyyar PDP ta sake zaɓen Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa bayan ya doke tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, a zaɓen fidda gwani.

A babban zaɓen shekarar 2023, Atiku ya zo na biyu bayan Bola Ahmed Tinubu, wanda ya lashe zaɓen.  Bayan bayyana sakamakon, Atiku tare da sauran ‘yan takarar adawa sun buƙaci a sake gudanar da zaɓen.

A shekarar 2025, Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma African Democratic Congress (ADC) tare da tsohon abokin hamayyarsa, Peter Obi.

Sai dai a karshe jami’iyyar ADC ta tsaida Atiku a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a zaben shekara ta 2027.

 

Peter Obi

An haifi Peter Onwubuasi Gregory Obi a ranar 19 ga Yuli, 1961 a Onitsha, Jihar Anambra. Ya yi karatun sakandare a Christ the King College, Onitsha, sannan ya wuce Jami’ar Najeriya da ke Nsukka. Ya fara aikinsa a harkar banki kafin ya shiga siyasa kai tsaye bayan ya tsaya takarar gwamnan Jihar Anambra a zaɓen 2003 a ƙarƙashin jam’iyyar APGA.

A zaɓen 2003, an ayyana Chris Ngige a matsayin wanda ya yi nasara, amma daga baya kotu ta soke nasarar Ngige tare da ayyana Peter Obi a matsayin wanda ya lashe zaɓen. Ya fara mulki a ranar 17 ga Maris, 2006.

A ranar 2 ga Nuwamba, 2006, majalisar dokokin Jihar Anambra ta tsige shi daga mukamin gwamna bisa zargin “munanan laifuka na rashin da’a a mulki”.

Mataimakiyarsa, Virginia Etiaba, ta maye gurbinsa, inda ta zama mace ta farko da ta zama gwamna a Najeriya.

Daga baya kotu ta dawo da Peter Obi kan mulki a ranar 9 ga Fabrairu, 2007. A ranar 17 ga Maris, 2010, aka sake zaɓensa a karo na biyu, kuma ya kammala wa’adinsa a ranar 17 ga Maris, 2014, lokacin da ya miƙa mulki ga sabon zaɓaɓɓen gwamna, Willie Obiano.

A shekarar 2019, Peter Obi ya nemi takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP tare da ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar. Sai dai sun sha kaye a hannun Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.

A shekarar 2022, Obi ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar Labour Party. A lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, Patrick Utomi ya janye takararsa domin ya ba Obi damar zama ɗan takarar shugaban ƙasa.

Ya sake fitowa Takara a 2023 inda ya zaɓi Yusuf Datti Baba-Ahmed a matsayin abokin takararsa. Sai dai sun sha kaye a hannun Bola Tinubu da Kashim Shettima na APC.

Gangamin neman zaɓen Obi ya samu karɓuwa musamman daga wani rukuni na magoya bayansa da ake kira “Obidients”, waɗanda suka nuna goyon baya sosai ga manufofinsa.

A ranar 2 ga Mayu, 2026, Obi ya yi sauya sheƙa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC). Daga baya, a ranar 29 ga Mayu, 2026, aka amince da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027 tare da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *